"" /> HADEJIA A YAU!: TARIHIN RAYUWAR SHEIKH JA'AFAR M. ADAM

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Friday, June 22, 2012

TARIHIN RAYUWAR SHEIKH JA'AFAR M. ADAM


An haifi marigayi Sheikh
Ja'afar Mahmoud Adam a
garin Daura, a shekara ta 1962
(ko da yake wani lokacin
yakan ce 1964).
Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara
karatunsa na allo a gidansu, a
wurin mijin yayarsa, Malam
Haruna, wanda kuma dan
uwansu ne na jini. Daga nan
kuma sai aka mayar da shi
wajen wani Malam Umaru a
wani gari wai shi Koza,
kimanin kilomita 9 a arewa da
Daura, wanda shi ma akwai
dangantaka ta jini a tsakanin
su, wanda kuma shi ne
musabbabin zuwansa Kano.
Bayan sun zo Kano ne tare da
wannan malami nasa, a
shekara ta 1971 (ko 1972), sai
suka zauna a makarantar
Malam Abdullahi, wanda
asalinsa mutumin jamhuriyar
Nijar ne, amma yake zaune a
unguwar Fagge a Kano. Tun
kafin zuwansu Kano, tuni
marigayi Sheikh Ja'afar ya riga
ya fara haddar Alkur'ani mai
girma, wanda ya kammala a
shekara ta 1978.
Bayan da Malam ya kammala
haddar Alkur'ani mai girma,
kasancewarsa mai sha'awar
ilimi, sai ya shiga makarantu
biyu a lokaci daya a shekara
ta 1980. Ya shiga makarantar
koyon Larabci ta mutanen
kasar Misra a cibiyar yada
al'adun kasar Misra, (Egyptian
Cultural Centre), sannan
kuma ya shiga makarantar
manya da ba su yi boko ba ta
Masallaci Adult Evening
Classes, tunda a lokacin
shekarunsa sun wuce shekaru
na primary, amma duk da
haka a wannan lokaci shi ne
mafi kankanta a ajinsu. Haka
ya rika yin wannan karatu
guda biyu: Waccan
makarantar ya je ta da
daddare bayan sallar isha'i,
waccan kuma ta koyo harshen
larabcin da yamma. Ya
kammala wadannan
makarantu a shekara ta 1983.
Wannan kuma shi ya ba shi
damar shiga makarantar
GATC Gwale a shekara ta
1984, kuma ya kammala a
shekara ta 1988. A shekara ta
1989, malam ya sami gurbin
karatu a jami'ar musulunci ta
Madinah, a inda ya karanta
ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an,
wanda kuma ya kammala a
shekara ta 1993. Sannan kuma
Sheikh Ja’afar ya sami damar
kammala karatunsa na digiri
na biyu (Masters) a Jami’ar
Musulunci, A Oundurman Sudan.
Sannan kuma, kafin
rasuwarsa, ya riga ya yi nisa
wajen karatunsa na digiri na
uku, wato digiri da digirgir
(PhD), a Jami’ar Usman Dan
Fodiyo da take Sokoto.
Daga cikin malamansa na
ilimi, akwai malaminsa na
farko, mutumin kasar Masar,
Sheikh Abdul-Aziz Ali al-
Mustafa, da kuma Malam
Nuhu a unguwar Dandago,
wanda malam ya karanci ilimi
fikihun malikiyya da wadansu
littattafai na hadisi a gurinsa,
da kuma Malam Muhammad
Shehu, mutumin Lokoja,
wanda Malam ya karanci
nahawu da sarfu da balaga da
adab a wajensa. Akwai kuma
Sheikh Abubakar Jibrin
limamin masallacin Juma'a na
BUK, akwai kuma Dr. Ahmad
Muhammad Ibrahim shi ma na
jami'ar Bayero ta Kano. Daga
cikin malamansa na jami'a
kuma, akwai Sheikh
Abdurrafi'u da Dr. Khalid
Assabt.
Daga cikin karatuttukan da
malam ya karantar da su, sun
hada da tafsirin Alkur'ani mai
girma, Kitabuttauhiid,
Umdatul Ahkaam, Arba'una
Hadiith, Kashfusshubuhaat,
Bulugul Maraam,
Riyaadussalihiin, Siiratun
Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz,
Siffatus Salaatun Nabiiy.
Wasu daga cikin daliban
malam sun hada da Malam
Rabi'u Umar R/Lemo da
Malam Sani Abdullahi
Alhamidi Dorayi da Malam
Abdullah Usman G/Kaya da
Malam Usman Sani Haruna da
Malam Ibrahim Abdullahi Sani
da Malam Ali Yunus
Muhammad da Dr. Salisu
Shehu da Malam Shehu
Hamisu Kura da Malam Anas
Muhammad Madabo.
Kafin rasuwarsa, malam ya
fara gagarumin aikin rubuce
tafsirinsa a harshen Hausa a
karkashin wannan cibiya
(Sheikh Ja'afar Islamic
Documentation Centre).
Marigayi Sheikh Ja'afar
Mahmoud Adam ya rasu ranar
juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428
(13/04/2007) sakamakon harin
da wadansu 'yan ta'adda suka
kai masa, a daidai lokacin da
yake jagorantar sallar asuba a
masallacin Juma'a na Dorayi.
Ya rasu ya bar mata biyu, da
'yaya shida, yayin da aka haifa
masa ta bakwai kwanaki 58
daidai bayan aiwatar da
wannan kisan gilla a kansa.
Dubun-dubatar mutane ne
daga ko'ina cikin kasar nan
suka halarci jana'izarsa, kuma
an binne shi ne a makabartar
Dorayi. Allah ya ji kan sa ya
gafarta masa, ya saka masa
da gidan aljanna. Amin

1 comment:

  1. Allah ya jikan mallam ya gafartamasa yasa al'janna fiddausi makoma

    ReplyDelete

RUBUTA RA'AYINKA!