Ranar Asabat 3-january-1999, Mai martaba Sarkin Hadejia Alh. Abubakar Maje Haruna ya Nada Alh. Adamu Abubakar A matsayin IYAN HADEJIA, NA FARKO. Kuma Ranar Laraba 11- september-2002, Allah ya yiwa Mai martaba Sarkin Hadejia Rasuwa. Alh. Abubakar maje Haruna.
TO A SAKAMAKON AMINCEWA DA GWAMNATI TAYI DA ZABEN 'YAN MAJALISSAR SARKI WATO (KING MAKER'S) Suka zabi Iyan Hadejia Alh. Adamu Abubakar maje a matsayin sarkin Hadejia, Na Goma sha shida (16). kuma an nada shi Ranar Asabat 14-september-2002. Bisa Al'ada ba'a kwana uku ba tare da an nada Sarki ba.
KUMA HAWANSA NA FARKO A MATSAYINSA NA SARKIN HADEJIA SHINE Hawan sallar Azumi wato A watan Disamba 2002. Sannan sallar Layya February 2002 Bai Hau ba saboda yaje Saudiyya.
29-March-2003.
A YAU ASABAT 29-March-2003 ANYI BIKIN BADA SANDA! An baiwa sarkin Hadejia Sanda a Karkashin shugabancin Gwamnan Jigawa ALH. IBRAHIM SAMINU TURAKI! A STADIUM TA HADEJIA.
Kuma bayan an Bashi Sandar jagorancin Kasar Hadejia A karkashin Tutar Shehu Usman Dan fodio, Mai martaba sarki yayi Hawa Guda Uku Wadanda suka Kayatar da
jama'ar Hadejia.
1, BIKIN GASAR ALQUR'ANI A SECONDARY FANTAI
2,TARON DA AKAYI A MAKARANTAR KOFAR AREWA
3,SAI HAWAN GANDU WANDA SHIMA YANA DA TARIHI A MASARAUTAR HADEJIA.
Hakiman da ya fara Nadawa sune:
1, DAN GALADIMA Alh.babbaji Adamu Hakimin waje
2, SARKIN DAWAKI Alh. Umar IbrahimHakimin kiri kasamma.
3, KATUKAN HADEJIA NA (2) BIYU Hakimin Turabu.
A gaba zan kawo muku Labarin Fitar sarkin Hadejia Rangadi da yayi da kuma Hakiman da a Nada.
Sarkin Hadejia magajin sambo allah ya ja zamanin sarki.
ReplyDeleteAllah yaja zamanin Sarki
ReplyDeleteAmeen! Muna godiya.
ReplyDeleteAllah ya karawa Sarki lafiya. Allah yaja zamanin Sarki.
ReplyDeleteAllah ya karawa maimartaba sarki lafiya.
ReplyDeleteSalam alaikum. Munajin dadin wagga shiri kwarai da gaske. Kuma muna rokon da a Bamu full tarihin daya daga cikin tarihin hakiman da sukai shahada da sarki Muhammadu. Wato madakin hadejia ahmadu kaura. Da kuma Ina descendent dinshi a yau?
ReplyDelete