"" /> HADEJIA A YAU!: WAKAR SAUDATU ADO BAYERO

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, July 8, 2012

WAKAR SAUDATU ADO BAYERO






1. Daren jiya ba na yau bane gun kwanan
yaro daban da bubba.

2. Bismillah zana shirya waka sarki Allah
kaban basira inyi wakar saude 'yar nikatau.

3. Ina dada godiya ga Allah sarki shi ya halicci saude.

4. Ga saude sarauniyar kano mai saukin kai ce da son mutane.

5. Ga mai fara'a da son mutane Bata gaji tsiya da tsangwama ba.

6. A kyauta ba kamar ki saude kanwar
sarkin kano na yanzu.

7. Kanwar Sarkin Bichi na yau Nasiru Ado dan uwan ki Saude. 

8. Ga mai haske kamar Azurfa Dadin suna kamar Tagullah.

9. Taurari ko suna da haske basu kai hasken farin wata ba.

10. Inda mata suna sarauta a kano sai mun nada ki saude.

11. A zaria sunyi Quen Amina muma a kano muna da saude.

12. A gabas na dangana da Borno ba
kyakkyawa kamarki saude.

13. A yamma najeni har Ilorin ni banga ba
wadda tayyi saude.

14. A nan kudu har zuwa Adamawa banga ba wadda tayi saude.

15. A arewa na dangana Nijar duka babu
Diyar da tayi saude.

16. Kai duk matan dake Kano nai jam'i duk ba kamar ki saude.

17. Hotonki ana comment akanshi na kirga Comment dubu a yanzu.

18. Ga allura cikin duhu sai mai zurfin
hankali ka tsinta.

19. Ga saude bakin zare a matoya sai mai
hankali ka tsinta.

20. Ni burina a duniya inga kina mulkin
kano sa'ade.

21. Allah ba yadda bai iya ba a zazzau shi ya bai Amina.

22. A Ingila ga Elizabeth nan Allah shi zaya baiwa Saude. 

23. Ansa giwa cikin zubo taci guda bakin
rabonta kelau.

24. Allah in yai nufi ga iko nai babu abinda
zai hana shi.

3 comments:

RUBUTA RA'AYINKA!