Hadejia A yau!
Daga M.MUHAMMAD IDRIS..
A cigaba da kawo muku Takaicaccen tarihin wadanda suka bada Gudunmawa a kasar Hadejia, yau mun tabo Mutum Uku wadanda tarihin Hadejia bazai manta dasu ba!
AIR VICE MARSHAL HAMZA ABDULLAHI(RTD)
*************** AVM Hamza Abdullahi. Daya daga manyan hafsoshin soja na kasa, daya
daga cikin manyan arewa, tsohon Gwamnan Jihar kano, tsohon ministan Abuja, tsohon
ministan aiyuka na musamman. Avm Hamza yayi mulki na wata 18 amma ya yi aiki na mamaki a fadin jihar kano.
Aiyukan da suka
shafi masarautar Hadejia sun hada da: ginin hanyar Bulangu da Guri, ginin Asibitin Birniwa, K/Hausa da Bulangu, ginin makarantun mata na kaugama da Birniwa, ginin kwaltocin cikin garin Hadejia da
gina fadar Hadejia ta zo daidai da
zamani. karin streets light. .
Lokacin yana ministan Abuja ko 'yan kwangila da dama sun
samu aiki, manyan mutane da yawa sun samu fulotai, ya samarwa matasa karatu a institute of management ta Abujan.
Avm Hamza bayan ya bar Gwamnati ya ci gaba da bayar da
gudunmawa domin ci gaban al'ummarsa ya gina katafaren gida domin saukar bakin kunya, ya gina masallaci na juma'a mahadi ka ture ya kuma tanaji makeken fili a yamma da masallacin domin gina makaranta, yana kawo
masu Likitocin ido domin masu larurin ido.
Avm yana daukan yara masu karamin karfi ya kaisu Turkish School in sun gama ya nema
musu admission a kasa ko a waje,yanzu haka akwai yara biyu a kasar Turkey wanda shi
yake daukan nauyinsu. Tsakanin Avm. da masarautarsa akwai kauna domin ba sallar da
za ta zo bai yi ta a Hadejia ba sai in ba ya kasa. Muna masa fatan alheri da karuwar
arziki mai amfani.
ALHAJI BELLO IBRAHIM AUYO
**************** Marigayi Alhaji Bello Ibrahim Auyo. "Agogo sarkin aiki" tsohon malamin makaranta, gogaggen dan siyasa. Ya fara aiki tun daga malamin makaranta har ya kai mukamin sakataren ilmi.
Ya rike mukamin kwamishinan zabe tun muna jihar kano. Ya yi
shugabancin karamar hukumar Hadejia har sau biyu. Shi ne shugaban ALGON na kasa.
Alhaji Bello Ibrahim ya fi kowane shugaban karamar hukuma da aka yi a Hadejia aiyuka
na raya gari. Alhaji Bello Ibrahim ne ya gina sakatariyar karamar hukumar Hadejia da ake
cikinta, shi ne ya gina Asibitin Kofar Arewa da shagunan bayanta, shi ne ya gina kasuwar jan bulo. Bello ya dauki ma'aikata da malaman makaranta masu yawa a zamaninsa.
A zamaninsa matasa masu yawa sun samu muhalli domin ya raba filaye da dama a wurare masu yawa.
Misali shi ya raba filin idi
kuma ya sanyawa wurin suna Unguwar Mu'azu Hadejia,
ya bayar a fanisau kuma shi
ya sayarwa mutane gidajen fanisau, ya raba a gabari, ya raba a Gandun Sarki.
Bello ya yi ginan magudanan ruwa ba adadi a Hadejia. Yayi aiyuka a Auyo lokacin muna hade da ita.
"Turmin tsakar gida sha
gwagwarmaya"
Bello mutum ne mai riko da addini, jam'i ba ya wuce shi, ya rike dangi musamman marayu, da azumi a bakinsa Allah ya karbi ransa. Allah ya sa ya sha ruwa a
Aljanna, ya yafe masa kura-kuransa.......
ALHAJI ADAMU KWANO ***************
Alhaji Adamu kwano tsohon ma'aikacin lafiya ne wanda ya bayar da gudun mawa matuka a
wannan fage. Allah ya yi masa fikira kwarai domin shi ba likita ba ne amma yakan yi aikin
da ya gagari likitoci.
Adamu kwano ya shahara akan kaciya domin galibin matasan Hadejia da
kewaye daga 'yan shekara 30 zuwa 50 duk yawanci shi ya musu shayi.
Alhaji Adamu kwano attajiri ne mai son ci gaban addini, shi ne ya
gina makarantun islamiya ta Hudu da Garko da makarantar sakandire ta Aminu Yusuf.
Adamu kwano shi ne mutum na farko da ya yi kokarin gina Asibiti mai zaman kanta sai dai ba ta fara aiki ba Allah (SWT) ya yi masa
rasuwa.
Muna rokon Allah(SWT) ya ji kansa yaarzurta mu da masu hali irin nasa. AMEEN.
No comments:
Post a Comment
RUBUTA RA'AYINKA!