HADEJIA A YAU!
AN RATAYA WA SARKIN KANO SUNUSI LAMBAR GIRMA TA K.B.E.
MADOGARA...
Gaskiya Ta fi Kobo
EAP/485-11-397
AN RATAYA WA SARKIN KANO SUNUSI LAMBAR GIRMA TA K.B.E.
A cikin watan Satumba/1958, bubban Razdan na Kano Sir. Gawain Bell ya ratayawa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi lambar Girma ta K.B.E. anyi gagarumin Hwan Daba inda aka kewaya gari daga nan aka nufo Ƙofar Fada inda anan ne aka ratayawa Sarki wannan lamba. Mutanen da sukayi kallon Dabar sun kwatanta ta da Dabar da aka yiwa Sarauniya. Sarakunan Ƙasar nan da yawa da manyan Ma'aikatan Gwamnati ne suka halarci wannan taro, a cikinsu harda Firimiyan Jihar Arewa Sir. Ahmadu Bello da Ministocinsa, har ma da Mukaddashin firayim Minista Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa.
Kimanin mutane Dubu Talatin (30,000) ne suka halarci taron shagalin Baiwa Sarki Sunusi wannan lambar Girma, ciki da wajen Jihar Arewa, abin sha'awa Sarkin Musulmi Sir. Abubakar da ya halarci taron ance rabonsa da Kano shekara 16 kenan. Firayim Minista bai samu zuwa ba amma Muhammadu Ribadu ya wakilce shi. Cikin manyan Baƙi harda Chif Jojin Sudan wadda Gwamnatin Arewa ta gayyato domin binciken Al'amuran Shari'ah a wannan Jiha, da kuma Wakilin Amurka a Nijeriya. Bayan an kimtsa duk manyan Baƙi sun zauna a Cikin Ƙwatattun Rumfuna sai Gwamnan Arewa ya nufo Ƙofar Mata inda aka je aka taryoshi akan Dawaki, Sarkin Kano da Hakimai da mahaya Dawaki duk aka tafi taryen Gwamna. Bayan sun gaisa da Sarki shima Gwamna sai ya hau Doki aka nufi ƙofar Kudu inda ake Shagalin bikin, ‘yan Doka masu Badujala ne suka share musu hanya suna tafe suna kiɗa da busa, Gwamna na tafe tare da Muƙaddashin Razdan na Kano Mr. melinctock. Sarki kuma na biye dasu da Dogarai da ‘yan Sulke da ‘yan Kwalkwali har zuwa ƙofar Kudu.
Sarkin Musulmi Abubakar tare da Sarkin Gwandu sune suka kai Sarki Sunusi Rumfar da za’a rataya masa Lambar Girman, daga nan sai Razdan ya miƙe ya karanta saƙon Sarauniya na bayar da Lambar, sannan sai Gwamna ya miƙe ya Ratayawa Sarkin Kano Sunusi lambar, sai wuri ya kaure da Tafi da shewa da kiɗe kiɗe da Bushe bushe don murna.
WANNAN DARAJA TA KOWA CE.
Sarkin Kano Sunusi ya miƙe yayi jawabi inda ya fara da godewa Allah (swa), sannan yace “Ina godiya ga Allah wadda da ikonsa ne wannan abu ya kasance a rana irin ta yau, sannan ina ƙara godiya ga Mai Martaba Sarauniya saboda wannan Daraja da ta bani, tare da shaidar Amincewa a rataya min a gaban Jama’a. Wannan Daraja ta shafi kowa ba ƙasar Kano kawai ba, harda duk Jihar Arewa. Na tabbatar da wannan shine lokaci na biyu da aka bada irin wannan Lambar girma a Jihar Arewa, mu duka munyi farin ciki da Alfahari a lokacin da Sarkin Ingila King George na 6 ya baiwa Sarkin Musulmi irin wannan lambar, to ina Alfahari da cewa nine na Biyu da aka baiwa wannan lamba, nayi Alƙawari zanyi matuƙar ƙoƙarin da zan iya in nuna na dace da wannan lamba da aka bani.
ZAMA MASU ZUMUNCI DA INGILA.
Da Sarkin Kano Sir. Muhammadu Sunusi ya Juyo wajen Maganar Samun Mulkin Kai sai yace, "Yau saura watanni goma sha takwas 18, muke zaton samun cikakken mulkin kai na Nijeriya. Mun lura da irin wahalce wahalcen dake gabanmu, amma duk lokacin da na hangi waɗannan wahalce wahalce nakan ji daɗi idan na tuna ƙasar nan zata zama ɗaya daga cikin ƙasashen da suke haɗa kai da Ingila. Da taimakonsu da kuma Jagoransa, in Allah ya yarda ƙasarmu zatayi ta ci gaba da Arziƙi."
Bayan Sarkin Kano Sunusi ya gama Jawabi sai aka Sallami kowa, duka manyan Baƙi suka tafi masauƙi. Da daddare kuwa Jam'iyyar NPC ta shirya wata ƙasaitacciyar rawa a Randabu Hotel saboda murnar bayar da lamba girma ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi. Alhaji Mai-wada M.H.A. shine ya shugabanci bikin Rawar.
MADOGARA...
Gaskiya Ta fi Kobo
EAP/485-11-397
No comments:
Post a Comment
RUBUTA RA'AYINKA!