"" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Tuesday, March 19, 2013

TAURARINMU (HADEJIAWA) Part two (2)

Image Hosted by ImageTitan.com Hadejia A yau! Daga M.MUHAMMAD IDRIS.. A cigaba da kawo muku Takaicaccen tarihin wadanda suka bada Gudunmawa a kasar Hadejia, yau mun tabo Mutum Uku wadanda tarihin Hadejia bazai manta dasu ba!


AIR VICE MARSHAL HAMZA ABDULLAHI(RTD) *************** AVM Hamza Abdullahi. Daya daga manyan hafsoshin soja na kasa, daya daga cikin manyan arewa, tsohon Gwamnan Jihar kano, tsohon ministan Abuja, tsohon ministan aiyuka na musamman. Avm Hamza yayi mulki na wata 18 amma ya yi aiki na mamaki a fadin jihar kano.


Aiyukan da suka shafi masarautar Hadejia sun hada da: ginin hanyar Bulangu da Guri, ginin Asibitin Birniwa, K/Hausa da Bulangu, ginin makarantun mata na kaugama da Birniwa, ginin kwaltocin cikin garin Hadejia da gina fadar Hadejia ta zo daidai da zamani. karin streets light. .


Lokacin yana ministan Abuja ko 'yan kwangila da dama sun samu aiki, manyan mutane da yawa sun samu fulotai, ya samarwa matasa karatu a institute of management ta Abujan.


Avm Hamza bayan ya bar Gwamnati ya ci gaba da bayar da gudunmawa domin ci gaban al'ummarsa ya gina katafaren gida domin saukar bakin kunya, ya gina masallaci na juma'a mahadi ka ture ya kuma tanaji makeken fili a yamma da masallacin domin gina makaranta, yana kawo masu Likitocin ido domin masu larurin ido.


Avm yana daukan yara masu karamin karfi ya kaisu Turkish School in sun gama ya nema musu admission a kasa ko a waje,yanzu haka akwai yara biyu a kasar Turkey wanda shi yake daukan nauyinsu. Tsakanin Avm. da masarautarsa akwai kauna domin ba sallar da za ta zo bai yi ta a Hadejia ba sai in ba ya kasa. Muna masa fatan alheri da karuwar arziki mai amfani.



ALHAJI BELLO IBRAHIM AUYO **************** Marigayi Alhaji Bello Ibrahim Auyo. "Agogo sarkin aiki" tsohon malamin makaranta, gogaggen dan siyasa. Ya fara aiki tun daga malamin makaranta har ya kai mukamin sakataren ilmi.


Ya rike mukamin kwamishinan zabe tun muna jihar kano. Ya yi shugabancin karamar hukumar Hadejia har sau biyu. Shi ne shugaban ALGON na kasa.


Alhaji Bello Ibrahim ya fi kowane shugaban karamar hukuma da aka yi a Hadejia aiyuka na raya gari. Alhaji Bello Ibrahim ne ya gina sakatariyar karamar hukumar Hadejia da ake cikinta, shi ne ya gina Asibitin Kofar Arewa da shagunan bayanta, shi ne ya gina kasuwar jan bulo. Bello ya dauki ma'aikata da malaman makaranta masu yawa a zamaninsa. A zamaninsa matasa masu yawa sun samu muhalli domin ya raba filaye da dama a wurare masu yawa.

Misali shi ya raba filin idi kuma ya sanyawa wurin suna Unguwar Mu'azu Hadejia,


ya bayar a fanisau kuma shi ya sayarwa mutane gidajen fanisau, ya raba a gabari, ya raba a Gandun Sarki.

Bello ya yi ginan magudanan ruwa ba adadi a Hadejia. Yayi aiyuka a Auyo lokacin muna hade da ita.

"Turmin tsakar gida sha gwagwarmaya"
Bello mutum ne mai riko da addini, jam'i ba ya wuce shi, ya rike dangi musamman marayu, da azumi a bakinsa Allah ya karbi ransa. Allah ya sa ya sha ruwa a Aljanna, ya yafe masa kura-kuransa.......



ALHAJI ADAMU KWANO *************** Alhaji Adamu kwano tsohon ma'aikacin lafiya ne wanda ya bayar da gudun mawa matuka a wannan fage. Allah ya yi masa fikira kwarai domin shi ba likita ba ne amma yakan yi aikin da ya gagari likitoci.


Adamu kwano ya shahara akan kaciya domin galibin matasan Hadejia da kewaye daga 'yan shekara 30 zuwa 50 duk yawanci shi ya musu shayi.

Alhaji Adamu kwano attajiri ne mai son ci gaban addini, shi ne ya gina makarantun islamiya ta Hudu da Garko da makarantar sakandire ta Aminu Yusuf.

Adamu kwano shi ne mutum na farko da ya yi kokarin gina Asibiti mai zaman kanta sai dai ba ta fara aiki ba Allah (SWT) ya yi masa rasuwa.

Muna rokon Allah(SWT) ya ji kansa yaarzurta mu da masu hali irin nasa. AMEEN.

Monday, March 18, 2013

TAURARINMU (HADEJIAWA) Part One (1)

Image Hosted by ImageTitan.comHadejia A yau! DAGA MUHAMMAD IDRIS HADEJIA


Shirin Taurarinmu zai Rinka tabo takaicaccen Tarihin Mutanen Kasar Hadejia da Irin ci gaban da suka bata, Domin kaima ka bada taka Gudunmawa. Kuma zamu fara da takaicaccan Tarihin.......


ALHAJI HAMZA TURABU *************** Alhaji Hamza Turabu. Bahadeje mazaunin kano. Alhaji Hamza tsohon ma'aikaci ne a Hukumar Aikin Gona ta Jiha. Yana rike da mukamin Director Forestry tun muna kano har muka zo jigawa kuma akansa ya bar aiki.

Dattijo ya yi wa mutane da yawa hanyar samun aiki musamman a Ma'aikatar Aikin Gona kuma shi ne ya assasa filantaishin masu yawa da muke gani a yau fadin kano da jigawa.

Alhaji Hamza mutum ne mai son ya ga matasa sun yi karatu shi ya sa gidansa ya zama mazaunin Dalibai 'yan wannan masarauta har a yau. Hadejawa suna ma addu'a Allah ya albarkanci zuriyarka. Amin.


SHEIKH MUHAMMAD LAMIN KHAN (MALAM MODIBO YALLEMAN) **************** Marigayi Sheikh Muhammad Lamin Khan yana daya daga cikin dattijon 'Yalleman, daya daga cikin malaman addini na wannan masarauta, shine bubban Limamin 'Yalleman.


Malam Modibo ya zaga kasashen Afirka da dama akan neman ilmin addini kuma ya same shi domin ya karantu a bangarori na addini dabam-dabam. Ana zuwa har daga garuruwan makwabta a dauki karatu a wurinsa.


Bayan kasancewar gidansa makaranta ce shi ne ya assasa Makarantar firamare ta Madani da kuma Sakandiren Madani. Matasa da yawa cikin garuruwan 'Yalleman, Dakayyawa, Hadiyin, Ubba, da kewaye a wannan makaranta suke karatu. Malam Modibo ya hada duk wani hali na dattako da ake so,don haka yake da girma a idon jama'a a ciki da wajen wannan masarauta.


Muna addu'a Allah ya sa kur'ani ya cece shi. Amin.


HAJIYA LAMI AMINU KANI *************** Hajiya Lami Aminu Kani 'ya ce a wurin Sarkin Fulanin Hadejia Alhaji Daudu Saleh. kuma matar na hannun daman AVM Hamza Abdullahi, wato Alhaji Aminu Kani. Hajiya Lami tana daya daga cikin tsofin 'yan boko mata na wannan masarauta.


Hajiya Lami babbar ma'aikaciya ce a hukumar bayar da wuta "PHCN" Kuma zamanta a wannan wuri ya amfanar da wannan masarauta matuka domin idan ka kasa masu aiki a PHCN na wannan masarauta kashi dari Hajiya Lami ce ta kai kashi saba'in daga cikinsu PHCN. Mace mai kamar maza.


Hadejawa sun baki Sarkin Fulanin Mata. Muna addu'a Allah ya kara daukaka. Amin.