Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Thursday, July 5, 2012

SARKIN HADEJIA BUHARI DA WAZIRIN SOKOTO A KATAGUM KASHI NA (2)

Image Hosted by ImageTitan.com HADEJIA A YAU!

A kashi na farko kunji yanda Buhari suka kare da Wazirin sokoto da Mutanen Katagum: da kuma komawar sarki Buhari shabawa wato iyakar Hadejia da Gumel da kuma Damagaram.

YAKIN TAKOKO:- Bayan an Nada Ahmadu a matsayin Sarkin Hadejia, sauran Magoya bayan Buhari sai suma suka bar Hadejia suka koma Shafowa inda Buhari yake suka zauna tare. Sarkin Hadejia Buhari anan ya zauna tsakanin Takoko da Shafowa a Arewacin Hadejia da mutanensa kuma yake tafiyar da wannan yankin. Kuma iyakar Hadejia ce da Damagaram da Machina ta Arewa maso Gabas wato yankin Niger da kuma Borno. Kuma Buhari ya bada Gudun mawa sosai a wannan Yankin wajen Maidasu Musulmi. Inda yayi ta jihadinsa a yankin, kuma a wannan zama da yayi a Shafowa Buhari ya samu kyakkyawar dangantaka da Sarkin Machina da kuma Shehun Borno Umar wanda ya mulki Borno a wannan shekara (1835-1880) wannan dangantaka ta kara baiwa Buhari karfin gwiwa.


A shekarar 1851, Sarkin Musulmi Alu Bubba ya yanke shawarar daukan matakin Karshe akan Buhari, saboda yana tunanin Shehun Borno zaiyi amfani da Buhari ya rusa Daular Sokoto saboda ya zame musu Barazana a Arewa Maso Gabas. A wannan lokacin kuma DanGaladiman Sokoto ya hada Mayaka daga Hadejia,Kano,Katagum,Misau da Jama'are zuwa shafowa.

A wannan lokacin kuma Buhari ya fita kudu da shafowa shi da Sarkin Machina yana garin Takoko shida Jarumansa. A lokacinda Dangaladiman sokoto suka fito su yaki Buhari sai ya zabi Sarkin Jama'are Samboli ya jagoranci yakin, saboda shi ya fisu sanin Yankin. A ranar da zasu yaki buhari kuma a ranar Buhari ya shirya mamaye Garuruwanda suke kudu da Hadejia, sai aka hadu a Garin Takoko. Yayin da aka hadu aka gwabza fada Buhari yaci Galaba a kansu duk suka gudu, Sarkin Hadejia Ahmadu yayi kokarin ya Gudu Kasar Kano amma sai Barde Risku ya bishi ya Kashe shi.

Bayan Yakin Takoko yazo karshe kuma an kashe Sarkin Hadejia Ahmadu Amma ba'a son ran Buhari ba kuma aka masa Sallah aka kaishi Hadejia aka binne shi, sannan sai Buhari ya koma Hadejia yaci gaba da Mulki. Sakamakon wannan yakin, dangantaka ta sake baci tsakanin Hadejia da Sokoto, kuma Sarkin Musulmi yaki yarda da ya nada Buhari Sarkin Hadejia. Sai ya nada Tukur Na yayari, kanin Sarki Ahmadu kuma yace ya zauna a Mashama a Kasar Katagum a Matsayin sarkin Hadejia ya Gaji wansa Ahmadu. Amma Tukur bai yarda ya zama Sarkin Hadejia ba saboda yana tsoron Buhari, sai yaga bazai iya yin haka ba. Kuma saboda Gudun kar Buhari ya kasheshi sai Tukur ya Gudu daga Mashema yayi kaura zuwa Kano Lokacin Sarkin Kano Usman Na1(1846-1855) Sai aka Turashi ya Mulki Yayari a Kasar Birnin Kudu. (Yayarin Tukur) Tukur ya zauna acan Har zuwa lokacinda ya Mutu 1909. Buhari kuma yaci gaba da mulkin Hadejia yana kai hare hare a matsayin Jihadi Har saida yakai Gabasawa,Sankara,Ringim da Kuka kwance A Arewa maso yamma. A Kudu saida ya mamaye Kununu,Takalafiya, Kafin baka, Doma, Ruba, Itas da Kwanda. A Gabas kuwa saida ya Mamaye Babuwari, Kazura, Dawah, Gatare da Margadu. Saida Sarki Buhari ya fadada kasar Hadejia tafi Ko ina fadin Kasa a karni na19.

GAMON KAFUR:-

Tuesday, July 3, 2012

DAJIN DUHUN KARO A HADEJIA.



HADEJIA A YAU! 

DUHUN KARO:-duhun karo wani Daji ne dake kasar Hadejia kuma yafi yawa a Gabashin Hadejia. Wannan Daji daji ne mai Dimbin tarihi wadda duk wadda yake kasar Hadejia zaice maka haka ya taso yaga wannan Dajin. Hasali ma wadda ya kafa Hadejia (HADE) ni'imar wannan Daji ce tasa ya zauna a wannan yanki. Dajin Duhun Karo yana tafe ne da Ruwa a Gefensa sannan ga Itatuwa masu bin Danshin ruwa a gefen ruwan, Kuma wannan dajin ya taso ne tun daga Falgore yamma da Kano har ya dangana da komadugu ta Jihar yobe, sannan ya nufi Jihar Borno har zuwa Tafkin Chadi.

Wannan Daji ya kasu da yawa a Kasar Hadejia inda ya bazu kuma yafi girma da Ni'ima a Yankin Baturiya da Gabta da yankin Kadira har ya shiga zuwa Kasar Gorgaram.   Duk wadda ya saba bin hanyar kano ta Ringim zai ga wannan dajin musamman kwanar Auyo zuwa Hadin mai dan karofi inda nan ne ya fito har bakin titi musamman ma Burtalin fulani na Wajedu, sannan shine ya shiga Muhimbira har fateka zuwa Bubbar Riga yayi Gabas har Sansanin Sarkin Damagaram Tanemu. 


Na shiga wannan Dajin kuma banda kukan tsuntsaye da Namun daji babu abinda kake ji. Nayi tafiyar kilo meter takai biyar a cikin dajin, har saida ya Kaini Askandun fulani da Akurya, na gamu da wani Bafulatani mai suna Musa kuma na tambayeshi shekarar sa nawa a wannan dajin? Sai yace shima anan aka haifeshi, kuma yanzu shima yana da 'ya'ya wadanda ya haifa a wannan Dajin. Na tambayeshi ko zai bani labarin wannan dajin? Sai yace ya tashi yaga Kuraye suna zuwa suna razana musu shanu, kuma yace akwai Namun daji kamar Gada, Barewa, Bauna da dai sauransu. Amma tunda aka fara sarewa dajin sai sukayi nisa kuma da 'yan farauta da suka damesu. Yace Amma har yanzu akwai kananan Namun daji kamar Zomo, Guza, kuma wani lokacin ana samun Gada. Tsuntsaye kuwa dukda harbi da ake Har yanzu akwaisu da dama.
Dajin in ka shiga cikinsa baza kasan ana rana ba saboda tsabar Inuwa da take ciki kuma ga Ruwa a gefensa. Akasarin bishiyoyin da ke dajin farar kaya ce da kuma Bishiyoyi kamar su Danya, Darbejiya, Gabaruwa, Kirya, Kanya, Magarya,  da sauran bishiyoyi masu Ni'ima.


Kalu balenda wannan Daji yake fuskanta shine Sare saren Bishiyoyi da ake yi a cikinsa da kuma fadada Gonakai da makwaftan dajin sukeyi. Ta wani fannin kuma akan samun wasu suna kunna masa wuta. Amma dukda haka in ka shiga zai baka sha'awa. Na tambayi wani dattijo mai suna Garba Tandanu mai shekara 60, yace wannan dajin yasan lokacin da kuraye suke Hanasu zuwa Hadejia ta Rugar Isa inda sai sun zagaya ta Tuwankalta sannan zasuzo Hadejia Amma yanzu sai dai tsuntsaye da kananan namun daji. HADEJIA A YAU.

Sunday, July 1, 2012

KASAR HADEJIA ZAMANIN SARKI ADAMU




HADEJIA A YAU! Hadejia tana daya daga cikin Garuruwan da ke Karkashin Tutar shehu Usman Danfodiyo! Jama'ar Hadejia Akasarinsu fulani ne da Hausawa da Mangawa. Kuma Suna bin Addinin Musulunci ne. Idan muka tabo Tarihin Hadejia tun lokacin mulkin Habe zamuga cewa dama ko a wancan lokacin Addinin Musulunci ne addinin mutanen Hadejia sai dai dan abinda ba'a rasa ba. Kafin a jaddada addinin Musulunci lokacin shehu dan fodiyo sarakunan Habe ne suke Sarautar Hadejia, kuma anyi sarakuna da dama kamar (1)Baude(2)Musa(3)Abubakar. Bayan Malam Sambo ya karbo tuta karkashin jagorancin Sarkin fulani Umaru sai Hadejia ta koma Karkashin mulkin Fulani.
HADEJIA A YAU! A yau Hadejia ta zama wata fuskar kasuwanci a jihar Jigawa, domin duk abinda ka sani na sayarwa zaka samu a wannan gari. A shekaru Hamsin baya In ba ranar Kasuwar Garin ba wani abin bazaka samu ba. Allah ya albarkaci Hadejia da kayan Lambu Irinsu Tumatir, Tattasai, Attaruhu, da sauransu. Wadannan ana yinsu ko wane lokaci a Hadejia ba sai da damana ba. Saboda Albarkar kogi da Allah ya bamu. Haka kuma fannin kayan Abinci kamar shinkafa,Alkama,Masara. Duk ba sai da damina akeyinsu ba a Hadejia. Saboda Albarkar da Allah ya bamu ta kasar Noma mai kyau. Idan muka koma batun Amfanin Abinda ke cikin Ruwa Hadejia A kullum Tana Fidda kifi kimanin Na Naira milyan Biyu a takaice! Wani abu da yake shine Kalu bale a garemu shine.........

Saturday, June 30, 2012

GWAMNATIN JAR HULA. SAI KANO


HADEJIA A YAU! Tarihi shike maimaita kansa! Kamar yanda aka sani a da can mun san wasu dattijai wadanda kullum Adonsu shine: farar riga bakin takalmi da Jar hula. Bamu sani ba ashe adon nasu yana da fa'ida, ba wai suna yi bane dan kansu. A lokacin jamhuriya ta daya anyi jam'iyyun siyasa da dama a cikinsu har da NEPU. Kuma kowace jam'iyya tana da nata taken kuma tana da Tuta Irin tata. To ashe wannan adon da mukaga wasu daga cikin Dattijanmu sunayi ado ne mai ma'ana saboda suna cikin jam'iyyar NEPU. Kuma sun saka akidarta a ransu shi yasa suka maida adonsu irin na tutar jam'iyyarsu. Haka ma a jamhuriya ta biyu anyi jam'iyyu da dama a ciki harda P.R.P. Kuma su 'yan jam'iyyar NEPU sune suka kafa P.R.P. Dan haka sai suka sake saka alamarsu ta da can ta zama itace dai alamar P.R.P.
KWANKWASIYYA!
A shekarar 2011 Kano ta sake maimaita wannan tarihi karkashin Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso Inda ya dawo da wancan adon na 'Yan NEPU. Shima ya maida adonsa farar riga da Jar hula kuma hakan ya samu karbuwa ga jama'ar kano. Yanzu farin yadi da jar hula kasuwarsu tafi garawa ba wai kano kadai ba harda jigawa da Bauchi da Kaduna da Katsina. Sai dai da yawa masu saka Jar hula in ka tambayesu basu san Ma'anar Hakanba. Kawai dai sunga Kwankwaso yana sakawa.