"" /> HADEJIA A YAU!: 06/01/2012 - 07/01/2012

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Saturday, June 30, 2012

GWAMNATIN JAR HULA. SAI KANO


HADEJIA A YAU! Tarihi shike maimaita kansa! Kamar yanda aka sani a da can mun san wasu dattijai wadanda kullum Adonsu shine: farar riga bakin takalmi da Jar hula. Bamu sani ba ashe adon nasu yana da fa'ida, ba wai suna yi bane dan kansu. A lokacin jamhuriya ta daya anyi jam'iyyun siyasa da dama a cikinsu har da NEPU. Kuma kowace jam'iyya tana da nata taken kuma tana da Tuta Irin tata. To ashe wannan adon da mukaga wasu daga cikin Dattijanmu sunayi ado ne mai ma'ana saboda suna cikin jam'iyyar NEPU. Kuma sun saka akidarta a ransu shi yasa suka maida adonsu irin na tutar jam'iyyarsu. Haka ma a jamhuriya ta biyu anyi jam'iyyu da dama a ciki harda P.R.P. Kuma su 'yan jam'iyyar NEPU sune suka kafa P.R.P. Dan haka sai suka sake saka alamarsu ta da can ta zama itace dai alamar P.R.P.
KWANKWASIYYA!
A shekarar 2011 Kano ta sake maimaita wannan tarihi karkashin Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso Inda ya dawo da wancan adon na 'Yan NEPU. Shima ya maida adonsa farar riga da Jar hula kuma hakan ya samu karbuwa ga jama'ar kano. Yanzu farin yadi da jar hula kasuwarsu tafi garawa ba wai kano kadai ba harda jigawa da Bauchi da Kaduna da Katsina. Sai dai da yawa masu saka Jar hula in ka tambayesu basu san Ma'anar Hakanba. Kawai dai sunga Kwankwaso yana sakawa.

Wednesday, June 27, 2012

KANO GARIN ALHERI.


HADEJIA A YAU! Kano ba gari ba Dajin Allah Inji masu iya magana! Tarihin kano abu ne wanda sai dai ace an baka kadan daga cikinsa, domin tarihinta bazai kammalu ba ga duk mai rubuta shi. An kafa kano tun a farkon karni na biyar bayan haihuwar Annabi Isah (AS) wato 500AD. Idan akayi la'akari da zuwan Bagauda da mutanensa. Tun daga wannan lokacin ake mulkin kano kawo yanzu mulkin fulani.
Kano ta shahara ta fannoni daban daban kama daga Ilmin Addini da na boko da kuma Uwa uba kasuwanci wanda ta zama babu kamarta a duk jihar Arewa. Al'adunsu da dabi'unsu abin koyi ne ga duk wanda yayi mu'amala dasu. Allah ya albarkaci kano da Ni'imomi daban daban wadanda basu misaltuwa. Kasuwa kuwa duk abinda ka sani ana sayarwa a duniya zaka samu a Kano, kuma duk abinda kake sayarwa zaka samu masu saye.
Kano ta zama wata cibiya ce wanda duk abinda ya sameta lalle ya samu duk jihar Arewa baki daya. A watannin baya ne kano ta samu kanta a wani hali wanda bata taba zatonsa ba. Wato na hare haren bom da kashe kashen jama'a wanda hakan ya kawo cikas a al'amuran yau da kullum. Amma duk da haka ba'a fasa saye ana sayarwa ba kamar yanda aka saba. Lalle duk abinda ya taba hanci to idanu zaiyi ruwa! Wato duk abinda ya taba kano to hakika ya taba Arewacin Nigeria.
Jama'ar kano da ma Arewacin Nigeria... Na rigingine fa ba-a fada masa ganin farin wata. Ina nufin mun san gurin wanda zamu kai kukan mu, shine sarkin da ya kafa kano ya albarkaceta da mutane Irin su WAZIRIN KANO, Da sauransu. Muna rokon Allah ya karemu daga duk abinda zai kawo barazana ga Kano da ma Arewacin Nigeria. Allah ka mana maganin abinda yafi karfinmu da abinda bamu zaton sa. Domin da ikonsa ne komai ya kasance da kuma abinda zai kasance. KANO KWARYAR KIRA MATATTARAR ALKAIRI. Daukar Nauyi freedom Radio kano.

TARIHIN SARAUTAR SARKIN HADEJIA NA (16)

Image Hosted by ImageTitan.com


Ranar Asabat 3-january-1999, Mai martaba Sarkin Hadejia Alh. Abubakar Maje Haruna ya Nada Alh. Adamu Abubakar A matsayin IYAN HADEJIA, NA FARKO. Kuma Ranar Laraba 11- september-2002, Allah ya yiwa Mai martaba Sarkin Hadejia Rasuwa. Alh. Abubakar maje Haruna.

TO A SAKAMAKON AMINCEWA DA GWAMNATI TAYI DA ZABEN 'YAN MAJALISSAR SARKI WATO (KING MAKER'S) Suka zabi Iyan Hadejia Alh. Adamu Abubakar maje a matsayin sarkin Hadejia, Na Goma sha shida (16). kuma an nada shi Ranar Asabat 14-september-2002. Bisa Al'ada ba'a kwana uku ba tare da an nada Sarki ba.

KUMA HAWANSA NA FARKO A MATSAYINSA NA SARKIN HADEJIA SHINE Hawan sallar Azumi wato A watan Disamba 2002. Sannan sallar Layya February 2002 Bai Hau ba saboda yaje Saudiyya.

29-March-2003.
A YAU ASABAT 29-March-2003 ANYI BIKIN BADA SANDA! An baiwa sarkin Hadejia Sanda a Karkashin shugabancin Gwamnan Jigawa ALH. IBRAHIM SAMINU TURAKI! A STADIUM TA HADEJIA.

Kuma bayan an Bashi Sandar jagorancin Kasar Hadejia A karkashin Tutar Shehu Usman Dan fodio, Mai martaba sarki yayi Hawa Guda Uku Wadanda suka Kayatar da
jama'ar Hadejia.

1, BIKIN GASAR ALQUR'ANI A SECONDARY FANTAI
2,TARON DA AKAYI A MAKARANTAR KOFAR AREWA
3,SAI HAWAN GANDU WANDA SHIMA YANA DA TARIHI A MASARAUTAR HADEJIA.

 Hakiman da ya fara Nadawa sune:
 1, DAN GALADIMA Alh.babbaji Adamu Hakimin waje 
2, SARKIN DAWAKI Alh. Umar IbrahimHakimin kiri kasamma.
3, KATUKAN HADEJIA NA (2) BIYU Hakimin Turabu.

 A gaba zan kawo muku Labarin Fitar sarkin Hadejia Rangadi da yayi da kuma Hakiman da a Nada.

Tuesday, June 26, 2012

RABE DA MUTANEN BORNO


HADEJIA A YAU!
Baramusa wani kauye ne a karamar hukumar Birniwa! Naje ziyara kauyen kuma ganin cewa duk barebari ne a garin, sai na samu damar in tambayi tarihin Rabe dan Fataralle. Na samu wani dattijo mai shekara 76, sai na tambayeshi tarihin Rabe. Kafin ya bani amsa saida ya tsinewa Rabe.
Yace wani mutumin sudan ne wanda ya Addabi bare bari tun daga kukawa Har zuwa Bedde. Sannan yace Rabe ne dalilin zuwansu nan kuma yace duk Babarbare ko bamangenda naganshi a Kasar Hadejia ko wani Guri, to lokacin Rabe ne suka Gudo nan. Yace kamar Kacallari,Kaigamari,kuka Ingiwa,Birniwa.kirikasamma,Jibori, da sauransu duk Gudun Rabe sukayi. A lokacinda Rabe yaje kukawa ya kashe duk mutanen Garin wasu da suka samu labari sai sukayi gudun hijira kasar Hadejia. Wasu kuma suka shigo cikin Hadejia kamar Gagulmari,Kakaburi,zonagalari,kilabakori da sauransu. Yace da can suna da zanen barebari amma yanzu sun canza sai suke zanen a kan fuskarsu wato uku uku. Sauran Labarin sai a Gaba.

Monday, June 25, 2012

GARKO DA SANA'AR SU. TUN KAFIN ZUWAN BATURE


HADEJIA A YAU! GARKKO Unguwar Garko Tana daya daga cikin unguwannin da suke Garin Hadejia, kuma Unguwa ce mai dimbin tarihi idan mukayi La'akari da Dadewarta. Garko tana daya daga cikin garuruwanda sarakunan Habe suka mulka a Hadejia amma A lokacin Gari ne mai zaman kansa kafin ya hade da Hadejia ya zama Unguwa. Kuma suna da sana'ar su wanda suka gada Iyaye da kakanni. Hakan ta bunkasa tattalin Arzikinsu tun a wancan lokacin zuwa yanzu. Sana'ar su Itace Amfani da kasa ko yumbu domin yin Randa,Gajirami,Tukunya,Tuli,Kula,Kasko,kafara da dai sauransu. Kuma wadannan kayan sune kayan da ake amfani dasu a kasar Hausa kafin zuwan Turawa. Domin Amfanin Gida wato Girki ko Aje ruwa ko makamantansu. Na samu wani Dattijo yana gina Randa a kofar gidansa Na tambayeshi ko A ina suke samun yumbun da suke gina randa? Yace duk a Hadejia suke samu akwai Mailolo ta Gabas da Hadejia anan suke samo yumbun da suke gina duk abinda nagani anan. Na tambayeshi ko shekara nawa yana yin wannan sana'a? Sai yace ya kai shekara Hamsin da biyu yana yi, kuma suna yi ne da Mahaifinsa da kannensa har zuwa yanzu ya zamanto shine bubba. Na tambayeshi menene dalilin da in an gina ake zuwa a gasa ta a wuta? Zan kawo muku karashen firar mu.

Saturday, June 23, 2012

JUMA'A RANAR ALKAIRI


Ranar jumaa itace mafi alherin dukkan wata
rana da rana ta fito a cikinta. cikinta Allah ya
halicci Adam, cikinta ne qiyama zata tsayu,
kuma ita ranar idi ice ga musulmai.Don haka
nema aka sharanta wasu abubuwa acikinta,
daga ciki akwai: hudubar jumaa, wanka,
fesa tirare, fita cikinta da mafi kyawun kaya
da yanayi me kyau, yin kabarbari lokacin fita
sallar, kusantar liman, da kuma tara tunani
gaba daya domin sauraren wa'azi da
ambato (wato huduba).

Friday, June 22, 2012

TARIHIN RAYUWAR SHEIKH JA'AFAR M. ADAM


An haifi marigayi Sheikh
Ja'afar Mahmoud Adam a
garin Daura, a shekara ta 1962
(ko da yake wani lokacin
yakan ce 1964).
Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara
karatunsa na allo a gidansu, a
wurin mijin yayarsa, Malam
Haruna, wanda kuma dan
uwansu ne na jini. Daga nan
kuma sai aka mayar da shi
wajen wani Malam Umaru a
wani gari wai shi Koza,
kimanin kilomita 9 a arewa da
Daura, wanda shi ma akwai
dangantaka ta jini a tsakanin
su, wanda kuma shi ne
musabbabin zuwansa Kano.
Bayan sun zo Kano ne tare da
wannan malami nasa, a
shekara ta 1971 (ko 1972), sai
suka zauna a makarantar
Malam Abdullahi, wanda
asalinsa mutumin jamhuriyar
Nijar ne, amma yake zaune a
unguwar Fagge a Kano. Tun
kafin zuwansu Kano, tuni
marigayi Sheikh Ja'afar ya riga
ya fara haddar Alkur'ani mai
girma, wanda ya kammala a
shekara ta 1978.
Bayan da Malam ya kammala
haddar Alkur'ani mai girma,
kasancewarsa mai sha'awar
ilimi, sai ya shiga makarantu
biyu a lokaci daya a shekara
ta 1980. Ya shiga makarantar
koyon Larabci ta mutanen
kasar Misra a cibiyar yada
al'adun kasar Misra, (Egyptian
Cultural Centre), sannan
kuma ya shiga makarantar
manya da ba su yi boko ba ta
Masallaci Adult Evening
Classes, tunda a lokacin
shekarunsa sun wuce shekaru
na primary, amma duk da
haka a wannan lokaci shi ne
mafi kankanta a ajinsu. Haka
ya rika yin wannan karatu
guda biyu: Waccan
makarantar ya je ta da
daddare bayan sallar isha'i,
waccan kuma ta koyo harshen
larabcin da yamma. Ya
kammala wadannan
makarantu a shekara ta 1983.
Wannan kuma shi ya ba shi
damar shiga makarantar
GATC Gwale a shekara ta
1984, kuma ya kammala a
shekara ta 1988. A shekara ta
1989, malam ya sami gurbin
karatu a jami'ar musulunci ta
Madinah, a inda ya karanta
ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an,
wanda kuma ya kammala a
shekara ta 1993. Sannan kuma
Sheikh Ja’afar ya sami damar
kammala karatunsa na digiri
na biyu (Masters) a Jami’ar
Musulunci, A Oundurman Sudan.
Sannan kuma, kafin
rasuwarsa, ya riga ya yi nisa
wajen karatunsa na digiri na
uku, wato digiri da digirgir
(PhD), a Jami’ar Usman Dan
Fodiyo da take Sokoto.
Daga cikin malamansa na
ilimi, akwai malaminsa na
farko, mutumin kasar Masar,
Sheikh Abdul-Aziz Ali al-
Mustafa, da kuma Malam
Nuhu a unguwar Dandago,
wanda malam ya karanci ilimi
fikihun malikiyya da wadansu
littattafai na hadisi a gurinsa,
da kuma Malam Muhammad
Shehu, mutumin Lokoja,
wanda Malam ya karanci
nahawu da sarfu da balaga da
adab a wajensa. Akwai kuma
Sheikh Abubakar Jibrin
limamin masallacin Juma'a na
BUK, akwai kuma Dr. Ahmad
Muhammad Ibrahim shi ma na
jami'ar Bayero ta Kano. Daga
cikin malamansa na jami'a
kuma, akwai Sheikh
Abdurrafi'u da Dr. Khalid
Assabt.
Daga cikin karatuttukan da
malam ya karantar da su, sun
hada da tafsirin Alkur'ani mai
girma, Kitabuttauhiid,
Umdatul Ahkaam, Arba'una
Hadiith, Kashfusshubuhaat,
Bulugul Maraam,
Riyaadussalihiin, Siiratun
Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz,
Siffatus Salaatun Nabiiy.
Wasu daga cikin daliban
malam sun hada da Malam
Rabi'u Umar R/Lemo da
Malam Sani Abdullahi
Alhamidi Dorayi da Malam
Abdullah Usman G/Kaya da
Malam Usman Sani Haruna da
Malam Ibrahim Abdullahi Sani
da Malam Ali Yunus
Muhammad da Dr. Salisu
Shehu da Malam Shehu
Hamisu Kura da Malam Anas
Muhammad Madabo.
Kafin rasuwarsa, malam ya
fara gagarumin aikin rubuce
tafsirinsa a harshen Hausa a
karkashin wannan cibiya
(Sheikh Ja'afar Islamic
Documentation Centre).
Marigayi Sheikh Ja'afar
Mahmoud Adam ya rasu ranar
juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428
(13/04/2007) sakamakon harin
da wadansu 'yan ta'adda suka
kai masa, a daidai lokacin da
yake jagorantar sallar asuba a
masallacin Juma'a na Dorayi.
Ya rasu ya bar mata biyu, da
'yaya shida, yayin da aka haifa
masa ta bakwai kwanaki 58
daidai bayan aiwatar da
wannan kisan gilla a kansa.
Dubun-dubatar mutane ne
daga ko'ina cikin kasar nan
suka halarci jana'izarsa, kuma
an binne shi ne a makabartar
Dorayi. Allah ya ji kan sa ya
gafarta masa, ya saka masa
da gidan aljanna. Amin

Thursday, June 21, 2012

SAKO ZUWA GA MASU AMFANI DA FACEBOOK


Malam Yusuf Audi, ya
rubuta cewa kamar haka...
Shafukan INTERNET da
Wayar hannu ta
GSM...... Bincike ya nuna
cewa shafin internet na
FACEBOOK da wayar hannu
ta GSM suna
daga cikin ababen dake
kara rura wutar
fadan addini a Nigeria.
Hakan yana faruwa
sakamakon irin yadda
mutane ke amfani da su
wajen isar da
sako atsakanin su.
Mutanen mu suna da son
bayar da labari,
ingantacce ko mara
inganci don neman
addu'ar 'yan uwansu ko
don nuna bajintar
su ko kuma don wata
manufa ta su ta
daban. Wannan yasa
dayawa sukan fidi abin da
ba
su da tabbas akan shi, ko
kuma suyi kari
cikin labarin na su. Ya kai
dan uwana me son bayar
da labari!
Kaji tsoron Allah, kada
kafadi, kada
karubuta sai abin da kaji
ko kagani ko
kuma kake da tabbas akan
shi. kasani za ka amsa
tamyar Allah akan abin
da kake fadi ko kuma kake
rubutawa
duniya(facebook), wacce
amsa katanada?
Ba wani abin birgewa
bane afara jin
labarin dake tayar da
hankali agurinka. Na ji
ance sun ce, wannan ba
dalili bane.
Addinin muslunci ya hore
mu da yin
magana ba tare da ILIMI
ba. Mu kiyaye ko Allah
(S.W.A) ya kiyaye mu. Ya
Allah! Kakiyaye mu,
kabamu zaman
lafia, amin.
To Jama'a sai mu kula da
fadar jita jita, domin karya
haramun ce. Allah ya kare
mu ameeeeeeeeen

Wednesday, June 20, 2012

MAI MARTABA SARKIN HADEJIA ALH.ADAMU A.MAJE

Image Hosted by ImageTitan.comHADEJIA A YAU! A Ranar Asabat 3/january/1999 Mai martaba Sarkin Hadejia Alh.Abubakar Maje Haruna ya Nada Alh.Adamu Abubakar A matsayin IYAN Hadejia.

kuma shine Iyan Hadejia Na farko a tarihin Hadejia!
kuma Ranar Asabat 20/september/2002 An nada Alh. Adamu Abubakar A matsayin Sakin Hadejia na Goma sha shida (16) karkashin jagorancin Galadiman Hadejia Alh.Habib Adamu.

kuma an nadashi a cikin fadar Hadejia. kwanaki Uku bayan Mutuwar Sarkin Hadejia Alhaji Abubakar Maje. yayi Hawan sallah na farko a Matsayinsa na Sarkin Hadejia wato:

Hawan sallar Azumi Dec. 2002. wato kafin a Bada Sanda. Ranar Asabat 29/March/2003 Akayi bikin bada sanda A filin wasa na Hadejia Karkashin Jagorancin Gwamnan Jigawa Alh.Ibrahim Saminu.

Ranar 14/september/2012 Zai shekara Goma(10) yana sarautar Hadejia.

zamu rinka kawo muku Irin Gudunmawa da ya bayar ta ci Gaban Wannan Masarauta. Daga yanzu har zuwa 14/september Na wannan Shekarar wato 2012. Hadejia A yau.

KADUNA BA LAFIYA


HADEJIA A YAU! Rahotanni daga jihar Kaduna ya nuna cewa Har yau rikici bai lafa ba dukda Dokar hana zirga zirga da aka sanya a Jihar. Ko a yammacin yau anji Karar harbe harbe da kone kone a yankin Badarawa,Unguwar yero da kuma wasu sassa a Unguwar Dosa. Wani ma'aikacin Gidan Redio ya ruwaito cewa An harbi wani yaro a Gabansa, Bayan an kaishi asibiti daga bisani ya cika. Allah ya mana maganin wannan masifa! Kwanaki hudu dai kelau ana zaman Dar dar a Jihar Kaduna Rikicinda ya rikide ya zama na kabilanci da Addini.

HADEJIA A YAU! A Ranar Laraba In Allah ya yarda zamu kawo muku Tarihin masallacin juma'ar Hadejia da yanda aka kafashi. daga bakin M.Mu'azu Hamza. zakuji a shekarar da aka kafashi da kuma lokacin wane sarki ne? kuma shekararsa nawa zuwa yau? Limamai nawa ne suka jagorance shi zuwa yau? A wane lokaci aka maidashi na siminti? da sauran abubuwan da ya kamata mu sani. Hadejia A yau.

Tuesday, June 19, 2012

KOFOFIN HADEJIA



HADEJIA A YAU! Wadannan Hoton kofar Gabas ne da Kofar Kudu. An Gina wadannan kofofi ne Tun kafuwar Hadejia kuma haka nan akayi ta gyaransu har zuwa yau. sai dai kash! sakamakon Biris da halin ko in kula ya jefa wadannan kofofi a cikin tsaka mai wuya. kamar kofar Gabas wani yanki daga cikinta tuni ya rushe. Haka Kofar kudu wato Cediyar kyalesu in kaje wucewa idan ba kula kayi ba bazaka san akwai kofa a gurinba. muna kira Ga Karamar hukumar Hadejia da Masarautar Hadejia da a taimaka a gyara wadannan kofofi kamar sauran kofofi 'yan-uwansu. Ganin cewa ba dan ana gyaransu ba da basu kawo yanzu ba. kuma muna kira ga Sarakunan kofofi da su rinka yiwa Karamar Hukuma tuni akai akai domin a gyara wadannan kofofin. Allah ya Daukaka Masarautar Hadejia. Hadejia A yau.

HADEJIA A YAU! An sake sanya dokar awa Ashirin da hudu a Jihar Kaduna Sakamakon Tashin hankalin da ya biyo bayan harin bom din da aka kai a Zariya da kaduna. An samu labarin Jiya da dadare matasa sunyi ta kai farmaki a junansu da niyyar daukan fansa. Haka kuma yau ma fada ya barke a Unguwanni daban daban a kaduna. Dukda dokar hana zirga zirga da Gwamnan jihar ya saka. A Damaturu ma ta jihar Yobe rikicin ya lafa kuma suma ansa dokar Hana zirga zirga. Mutanen garin dai sun bayyana wannan abin a matsayin Gazawar Gwamnatin tarayya na kasa magance matsalar tsaro.

KOFAR KUDU DA KOFAR AREWA



HADEJIA A YAU! Kofar kudu da kofar Arewa.

Monday, June 18, 2012

TASHIN BOM A DAMATURU DAGA BBC HAUSA

Rahotanni daga Damaturu babban
birnin jihar Yobe dake Arewacin
Najeriya, sun ce mazauna unguwanni
da dama ne suka tsere daga gidajen
su, yayin da wasu karin suka
kauracewa unguwannin su domin
samun mafaka.
Wannan dai ya biyo bayan tashin
bama bamai da karar bindigogin da
aka rika ji ne ba kakkautawa a
yammacin yau.
Rundunar Hadin Gwiwar Samar da
tsaro a jihar Yoben ta tabbatar da
abkuwar lamarin, sai dai ba ta
bayyana adadin asarar rayuka da
jikkata da aka samu ba a sakamakon
wannan hari.
Harin na Yoben dai na zuwa ne
kwana daya bayan wasu hare haran
kunar bakin wake da aka kai kansu
coci-coci uku a garin Kaduna da
kuma Zaria.
Hare haran da kungiyar Ahlisunna
lidda'awati wal jihad da ake kira
Boko Haram suka yi ikirarin kaiwa.

HADEJIA A YAU! Sarkin Hadejia Sambo shine ya karbo Tutar Musulunci a gun Usman Dan fodiyo! Yayi mulkin Hadejia tun daga 1808 zuwa 1848. Allah ya masa Rasuwa a Mai-Rakumi. Kuma anan kabarinsa yake! A cikin 'ya'yansa akwai wadanda sukayi Sarautar Hadejia a lokacin yana Raye. Kamar Garko Gambo 1845t-1847, Abdulkadir Dan Sambo 1847-1848. Sannan Sambo yaci Gaba da Mulkin Hadejia kuma ya Rasu a wannan shekarar. Sai kuma Dansa Buhari Sai Ahmadu sannan Buhari Sai jikansa Umaru Dan Buhari. Sai kuma Dansa Haru Bubba. Allah ya Gafarta musu.

KABARIN SARKIN HADEJIA SAMBO


HADEJIA A YAU! Sarkin Hadejia Sambo shine ya karbo Tutar Musulunci a gun Usman Dan fodiyo! Yayi mulkin Hadejia tun daga 1808 zuwa 1848. Allah ya masa Rasuwa a Mai-Rakumi. Kuma anan kabarinsa yake! A cikin 'ya'yansa akwai wadanda sukayi Sarautar Hadejia a lokacin yana Raye. Kamar Garko Gambo 1845t-1847, Abdulkadir Dan Sambo 1847-1848. Sannan Sambo yaci Gaba da Mulkin Hadejia kuma ya Rasu a wannan shekarar. Sai kuma Dansa Buhari Sai Ahmadu sannan Buhari Sai jikansa Umaru Dan Buhari. Sai kuma Dansa Haru Bubba. Allah ya Gafarta musu.

MAI GORIBA


HADEJIA A YAU! Wannan Hoton Mai Goriba ne! Kusa da Maskangayu Inda Turawa suka fara kafa sansaninsu kafin su Shigo Hadejia. Bayan sunci Hadejia da yaki kuma sai suka gina Bariki Ta zama nan ne Gidajensu da Ofis dinsu Har zuwa lokacinda Nigeria ta samu 'yancin kai a shekarar 1960.

KOFAR MANDARA


HADEJIA A YAU! Wannan kofar Talata ce ko kofar Mandara! Tana daya daga cikin kofofin Garin Hadejia. Ta wannan kofar ce Turawa suka shigo Hadejia a 1906. Kuma da can babu ita Turawa ne Suka fasa Ganuwar Hadejia Suka shigo Shine Dalilin da ake ce mata Kofar Talata saboda Ranar Talata Turawa suka fasa ta suka shigo Hadejia ta cikinta. Hadejia A yau.

KOWA YA GYARA YA SANI


HADEJIA A YAU!
Assalamu Alaikum! Bayan gaisuwa da fatan
Alkairi Ga 'yan wannan Masarauta, Muna
kara godiya ga Allahu subhanahu-wata'ala
da ya bamu ikon Rubuta wannan wasika.
Domin da Ikonsa ne Komai ya kasance da
kuma abinda zai kasance! Bayan haka Ina
kira ga shugabannin Hadejia da su taimaka
su Inganta mana Muhimman guraren
Tarihinmu na kasar Hadejia. Sakamakon
Lalacewa da suke kokarin yi. Kamar Tsohon
Gidan yari, Gulbin Atafi da Ramin zaki, bariki
wato Gidan Rasdan da na D.O., kabarin
Captain H.H. Phillips wato Mai Tumbi, Kofar
Kudu (chediyar kyalesu) da kuma kofar
Gabas. Wani mutum yazo daga BIDDA ta
jihar Niger yace min Yana so na kaishi
Kabarin Captain phillips, sai nayi shiru Ina
tunanin wanene captain phillips? Sai na tuna
lokacin muna yara In munje kanya muna
zuwa kabarin Mai tumbi. Kuma a jikin
kabarin an rubuta captain H.H.phillips! Sai
nace masa Muje ko da mukaje sai na fara
Gabatar masa da Bariki cewa a nan Turawa
suka fara zama. Sai yace dani A'a ai sun
Zauna a can Gaba kafin suzo nan. Nace Eh
hakane. Koda mukaje Kabarin Mai tumbi sai
muka ga Ginin duk ya rushe kabarin yana
nema ya bata. Sannan sai yayi kira ga
Hukumomi su rinka kawata Guraren Tarihi
Irin wadannan. To muma muna kira ga
wadanda abin ya shafa da su Gyara guraren
tarihi ba sai kabarin Mai tumbi kawai ba.
Sannan yace In kaishi Fantai Inda Gidajen
Sarakunan Habe suke. Ko da yake munje
Amma bamu samu Dagacin Mandara a gida
ba amma mun Dauki Hotunan Gidajen nasu
da kuma Tsangayar Gwani Gambo a cikin
'Yankoli. Sannan Muka Zarce zuwa Mai-
Rakumi mukayi Ziyara ga kabarin Sarkin
Hadejia Sambo. Bayan mun dawo Mukayi
sallama da Bako ya wuce Gogaram Ta Bade
Yace daga nan Zaije har Ngazargamu. Nace
Allah ya kiyaye hanya. Sannan sai na fara
tunani Ashe tarihi yana da muhimmanci? Sai
na tuna Ai malamin History yace:- History is
the systematic Account of past and present
Event. Zan baku Karashen Labarin anan
Gaba. Hadejia A yau.

Sunday, June 17, 2012

JIYA BA YAU BA.



HADEJIA A YAU!
Assalamu Alaikum! Bayan gaisuwa da fatan Alkairi Ga 'yan wannan Masarauta, Muna kara godiya ga Allahu subhanahu-wata'ala da ya bamu ikon Rubuta wannan wasika. Domin da Ikonsa ne Komai ya kasance da kuma abinda zai kasance! Bayan haka Ina kira ga shugabannin Hadejia da su taimaka su Inganta mana Muhimman guraren Tarihinmu na kasar Hadejia. Sakamakon Lalacewa da suke kokarin yi. Kamar Tsohon Gidan yari, Gulbin Atafi da Ramin zaki, bariki wato Gidan Rasdan da na D.O., kabarin Captain H.H. Phillips wato Mai Tumbi, Kofar Kudu (chediyar kyalesu) da kuma kofar Gabas. Wani mutum yazo daga BIDDA ta jihar Niger yace min Yana so na kaishi Kabarin Captain phillips, sai nayi shiru Ina tunanin wanene captain phillips? Sai na tuna lokacin muna yara In munje kanya muna zuwa kabarin Mai tumbi. Kuma a jikin kabarin an rubuta captain H.H.phillips! Sai nace masa Muje ko da mukaje sai na fara Gabatar masa da Bariki cewa a nan Turawa suka fara zama. Sai yace dani A'a ai sun Zauna a can Gaba kafin suzo nan. Nace Eh hakane. Koda mukaje Kabarin Mai tumbi sai muka ga Ginin duk ya rushe kabarin yana nema ya bata. Sannan sai yayi kira ga Hukumomi su rinka kawata Guraren Tarihi Irin wadannan. To muma muna kira ga wadanda abin ya shafa da su Gyara guraren tarihi ba sai kabarin Mai tumbi kawai ba. Sannan yace In kaishi Fantai Inda Gidajen Sarakunan Habe suke. Ko da yake munje Amma bamu samu Dagacin Mandara a gida ba amma mun Dauki Hotunan Gidajen nasu da kuma Tsangayar Gwani Gambo a cikin 'Yankoli. Sannan Muka Zarce zuwa Mai-Rakumi mukayi Ziyara ga kabarin Sarkin Hadejia Sambo. Bayan mun dawo Mukayi sallama da Bako ya wuce Gogaram Ta Bade Yace daga nan Zaije har Ngazargamu. Nace Allah ya kiyaye hanya. Sannan sai na fara tunani Ashe tarihi yana da muhimmanci? Sai na tuna Ai malamin History yace:- History is the systematic Account of past and present Event. Zan baku Karashen Labarin anan Gaba. Hadejia A yau.

WASIKA DAGA AJI KIMA ZUWA GA SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR HADEJIA

Free Web Proxy
Budaddiyar wasika ga mai girma shugaban karamar shukumar Hadejia da yan majalissarsa.
Bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci, ina mai farin
cikin rubutoma wannan takardar domin in nuna irin
goyan baya da nake bawa wannan jam'iya da wannan gwabnatin mai albarka, bayan haka ina jinjinama bisa irin kokarin da kake wajen ciyarwa da
wannan karamar hukuma gaba. Ina sake jinjinama da yadda kake gudanarwa da mulkinka cikin
kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Bayan haka ina so nayi amfani da wannan damar na tunatar da kai wasu muhimman abubuwa
wanda idan kayi su zasu taimakama wajen samin sahihiyar
hanyar ci gaba da kuma adana tarihi ko bayan
ranka, wannan abun kuwa sune kamar haka.
Kasancewar garin hadejia babban gari ne mai tsohon tarihi a jeri garuruwan Hausa to ya kamata
ace yau akwai abubuwan da zamu yi alfari da su wajen tarihi kamar yadda ya'u idan kaje Daura zaka tarar da abubuwan da suka faru shekaru dari uku ko hudu
da suka shude kamar yau akayi su.
Ma'ana muma a garin Hadejia muna da irin guraren
nan kamar kabarin mai tumbi, kofar mandara, ruwan Atafi, Rijiyar turawa, mabuga, majema, marina, bariki da sauransu.
Kuma ya kamata ana tunawa da mutanan da suka bawa wannan gari gudunmawa misali saka
sunayensu a titinah,dakin taro makarantu dasauransu. mutane irinsu Alh Haruna uji ya kamata a
na tunawa dasu, amma abin al'ajabi aka saka sunayen mutane a titinah aka manta da Haruna
uji, wanda ya bada muhimmiyar gudunmawa wajen daukaka masarautar hadejia.
Saboda haka a madadin daliban Hadejia emirate ina
mika wannan sakon ga maigirnma shugaban karamar hukuma da fatan za'a duba. Nagode.
Comrade Aji kima hadejia secretary general Hadejia student Association.

Thursday, June 14, 2012

MANYAN BORNO SUN ROKI DA A KAWO KARSHEN RIKICIN BOKO HARAM

HADEJIA A YAU! Al'ummar Jihar Borno dake Arewacin Nigeria sun Roki 'yan kungiyar Jama'atu Ahlussunna lidda'awati wal jihad wadda aka fi sani da suna Boko Haram da su Amince a tattauna dasu da Gwamnati domin a kawo karshen Hare harenda yake janyo Rasa rayuka da gidaje. A wata fira da yayi da 'yan jarida a Maiduguri Dr. shettima Ali Munguno ya bayyana rikicin boko haram a matsayin rikici ne wanda ya janyo Asarar rayukan Al'umma da gidaje, kuma ya janyo Rashin aikin yi ga Al'umma. Ya bayyana cewa mutane basu kwanciyar hankalin da zasu tafiyar da rayuwarsu a tsinake, ko harkokinsu na yau da kullum.uma ya bayyana cewa Jama'a basu samun salloli Biyar a cikin Jam'i saboda fargabar abinda zai kasance,Saidai mutum yayi sallarsa a cikin gidansa saboda rashin samun nutsuwa. Dr.Ali Munguno ya kara da cewa yana rokonsu da su Amince a tattauna dasu domin a kawo karshen Asarar rayuka da ake. yace a matsayinsu na 'yan kasa suna da ikon rayuwa a jikin mutane ba tare da tsangwama ba. yace duka mu da su kasarmu ce, bamu da wata kasar da tafi wannan. kuma ya kara da cewa Gwamnatin tarayya tare da gwamnatin Jiha a hada hannu wajen tattaunawar domin a kawo karshen wannan Al'amari.

Wednesday, June 13, 2012

SARKIN YAKIN SARKIN MUSULMI DA GOBIRAWAN MADARUMFA

SARKIN YAKIN SARKIN MUSULMI!

 Kamar yadda kuka gani A sama Zamu kawo muku Tarihin Zuwan Sarkin Marma Muhammadu Madarumfa. Iyakar sokoto da Niger da kuma yakin da akayi tsakanin Muhammadu da Gobirawan Madarumfa, akan kogin da ya raba Niger da Nigeria, kusa da Jibya. A zamanin Sarkin Musulmi Abubakar Atiku Na Biyu Sarkin Hadejia Muhammadu yaje Sokoto dashi da mutanensa lokacin yana Sarkkn Marma, koda yaje sai ya iske ana yaki tsakanin rundunar Sarkin Musulmi da kuma Gobirawan Madarumfa. Yaki yayi tsanani gashi Dawakai da mutanen Sarkin Musulmi suna jin Kishi su kuwa Gobirawa sun tsare Ruwa,  Koda Sarkin Hadejia Muhammadu yaga haka sai ya nemi izni ga Sarkin Musulmi don a bashi dama dashi da mutanensa su shiga wannan yakin. Bayan an bashi izni sai yacewa Sakkwatawa yanzu zaku sha Ruwa koda jini ya gurbatashi, haka kuwa akayi Sarkin Hadejia da jama'a tasa suka shiga sukayi ta dauki ba dadi da Gobirawan Madarumfa har saida sukaci galaba a kansu, suka kore na korewa suka kashe na kashewa suka kama wasu a mazaunin Bayi. Bayan an gama yaki Sarkin Hadejia Muhammadu yazo yayi gaisuwa ga Sarkin Musulmi yace masa Ruwa ya samu aje asha a baiwa Dawakai. Bayan an koma Sokoto sai Sarkin Musulmi ya nada Sarkin Hadejia Muhammadu a matsayin Sarkin yakin Sarkin Musulmi saboda irin gudunmawa da ya bada. 

Bayan nadinsa a matsayin Sarkin yakin Sarkin Musulmi sai yayi Sallama da Sakkwatawa suka rakoshi har kan iyaka tare da jama'arsa suka kamo hanya suka dawo Hadejia. Kafin Sarkin Hadejia ya iso gida har labari ya samu Hadejiawa cewa an nada Muhammadu Sarkin yakin Daular Usmaniyya, dan haka sai jarumai da mahaya sukayi shjri sukazo suka taryeshi. 

A gaba zamu baku labarin shigowarsa Hadejia  da yadda aka kaiwa Sarkin Hadejia Haru Bubba Labarin Muhammadu. Harda Asalin Jafi da ake Ran sallah A kusa da Masallacin Juma'a. Muhammadu na Allah Ruwan kogi Tafi sannu sannu Wanda yayi wargi Ya Halaka. Giwa ta gama da Masu Karfi Ta wuce.

Monday, June 11, 2012

TARIHIN RAYUWAR MARIGAYI UMARU MUSA 'YAR-ADUA


Umaru Musa Yar'Adua
Shi dai marigayi Malam Umaru Babangida
Musa 'Yar'Adua, an haifeshi ne a ranar 16
ga watan Augustan 1951 a birnin Katsina
dake arewacin Najeriya. Mahaifinsa shine
tsohon ministan birnin Lagos na farko a
jamhuriya ta farko, kuma kafin ya rasu
shine Matawallen Katsina, sarautar da
kuma shi ma marigayi Umaru Musa
'Yar'Adua ya gada.

Marigayin ya fara makarantar Firamare ta
Rafukka a 1958 kafin a mayar da shi
makarantar Firamare ta kwana dake
Dutsen Ma a 1962. Ya kuma halarci
kwalejin gwamnati dake Keffi daga 1965
zuwa 1969. Sai kwalejin Barewa 1971,
inda ya samu takardar shedar karatu ta
HSC.
Tsohon shugaba 'Yar'Adua ya halarci
Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya daga
1972 zuwa 1978 inda ya samu takardar
shedar digiri akan kimiyyar haÉ—a sinadirai
ko Chemistry da Malanta, kafin ya koma
domin samun babban digiri duk dai akan
kimiyyar ta Chemistry.

Marigayin yayi bautar
ƙasa a jihar Lagos inda ya koyar a wata
makaranta da ake kira Holy Trinity daga
1975-1976.
Bayan da ya kammala aikin yiwa ƙasa
hidima ya fara aikin Malanta gadan-gadan
a kwalejin share fagen shiga jami'a da ake
kira CAST dake Zariya a tsakanin 1976
zuwa 1979.

A shekarar 1983 marigayi
Malam Umaru Musa 'Yar'adua ya bar aikin
Malanta ya fara aiki da Gonar Sambo Farms
a Funtua dake jihar Katsina inda ya zama
GM daga 1983-1989.
Daga shekarar 1984 bayan da Sojojin
sukayi juyin mulki malam Umaru Musa
'Yar'adua an kira shi domin zama wakili a
hukumar gudanarwar kanfanoni da
hukumomin gwamnati da dama da suka
haÉ—a da hukumar samar da kayan Noma
da kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar
katsina, Bankin Habib da Hamada Carpets
da Madara Limited da kuma kanfanin buga
Jaridu da Mujalla ta The Nation wanda ke
kaduna kuma wansa Marigayi Janar Shehu
Musa 'Yar'Adua ya mallaka.


A lokacin da marigayi Malam Umaru Musa
'Yar'Adua ya shiga siyasa ya yi hannun riga
da mahaifinsa wanda a wancan lokaci yake
mataimakin shugaban Jam'iyar NPN, inda
shi kuma ya zama wakili a jam'iyar PRP ta
Malam Aminu Kano mai adawa da NPN. A
lokacin da Janar Babangida ya kaÉ—a gangar
siyasa ya zama sakataren jam'iyar SDP a
jihar ta Katsina kuma É—an takararta na
gwamna, amma kuma É—an takarar
jami'iyar NRC na wancan lokaci Malam
Saidu Barda ya kada shi.

To sai dai a 1999
Malam Umaru Musa 'Yar'Adua ya tsaya
takakarar muƙamin gwamnan jihar ta
Katsina kuma ya samu nasara a ƙarƙashin
jam'iyar PDP, haka kuma ya sake nasara a
zaɓen 2003.
A shekarar 2007 Umaru Musa 'Yar'Adua ya
zama ɗan takakar muƙamin shugaban
ƙasa na Jam'iyar PDP bayan ya samu
taimakon tsohon shugaban ƙasa Cif
Olusegun Obasanjo ya zama shugaban
ƙasa a ranar 29 ga watan Mayun 2007.
To sai dai rashin lafiya da tsohon shugaban
yayi fama da ita ta sanya bai samu sukunin
gudanar da harkokin mulki kamar yadda
yayi fata ba musanman ƙudirorinsa guda
bakwai daya tsara na ciyar da ƙasar gaba
kafin nan da ƙarni ta 2020.


Marigayi Malam Umaru Musa 'Yar'Adua ya
rasu a ranar 5 ga watan Mayun shekara ta
2010 da muke ciki a fadar gwamnati dake
Abuja watanni biyu bayan komowarsa gida
daga Saudiya inda yake jinya.
Ya kuma rasu ya bar mahaifiyarsa da
'yan'uwa da matar aure guda Hajiya Turai
tare da 'ya'ya bakwai da ya haifa da ita da
suka haÉ—a da mata biyar da maza biyu.
Haka kuma yana da wasu 'ya'ya biyu maza
da matarsa ta biyu Hajiya Hauwa Umar
Radda.

Thursday, June 7, 2012

ZUWAN TURAWA KASAR HADEJIA KASHI NA (2)


HADEJIA A YAU! A kashi na farko Na baku Labarin yadda Turawan mulkin mallaka suka yiwa Hadejia Leken Asiri, wadda hakan ta basu dama suka kama garin.

Yanzu zamu dora! Koda yake Sarkin Hadejia Muhammadu ya samu labarin Turawa sun ci Kano da Katagum duk sun koma karkashin mulkinsu yace da yabi Kafiri Gara yayi shahada,Turawa basu fasa ba shima bai fasa ba.

Ranar Talata 1906 Turawa suka shigo Hadejia Gadan gadan akayi ta gwabza fada, dukda dawakan Hadejia basu taba jin kukan Igwa ba da sunji wannan kukan sai su turje haka nan akayi ta fama da su. jama'ar Hadejia manya da yara kowa yayi shirin yaki haka nan akayi yaki har Zuwa Azahar,  kuma Turawa suna kara shigowa Hadejia, saboda makaman su ba irin namu bane. An kashe manyan fadawan Hadejia da hakimai:

kamar yadda na fada a baya Sarkin Hadejia Muhammadu saida aka ce masa Kada Hadejia ta kare saboda shi Tukuna ya rusuna har Turawa suka cim masa. Allahu akbar!

koda Hadejiawa suka samu labari an kashe sarki sai kowa ya Rusuna,  Turawa suka shigo Hadejia suka Fara shirin tafiyar da mulki irin nasu. Hadejiawa sukayi Jana'izar wadanda suka mutu, wadanda kuma sukaji rauni aka kaisu Gidajensu. Turawa suka Nada Sarkin Hadejia Haru mai karamba 1906. 

To akwai sarkin yaki cilin Yana daga cikin wadanda suka samu raunuka a yakin kuma shi Captai phillips ya sanshi dama can. to kullum sai yaje Gidan sarkin yaki Yana Masa Izgilanci yana ce masa ina yakin? Ashe Sarkin yaki yana jin ciwon hakan. Wata rana sai yacewa matarsa Idan zata Kawo masa Abinci tasa wuka a cikin Tuwon.

haka kuwa tayi. saida captain phillips yazo yana masa Izgili Sai yasa hannu kamar mai cin tuwo sai ya dauko wuka ya Burmawa captain phillips a tumbinsa ya kasheshi. Kabarinsa yana can a Gabas Da Bariki Hanyar Tandanu. Shi ake cewa Kabarin mai tumbi. Wadanda suka rasa rayukansu a yakin suna da dama Amma ga kadan daga Sunayensu. Muhammadu Sarkin Hadejia, Madacima shi suka fara kashewa, Galadima, Ma'aji salihu, Furya, Barwa da Tarno, Bori na Salihu, Kaura Amadu, Mabudi zakar, Jarma warkaci, Sabo jikan Tete, Dandalma, Abdulwahabu sarkin Baka, Sarkin Arewa, Alkali, Farau farau, Sarkin Dawaki Dan gazau, Da dai Sauransu! Allah yaji kansu da Rahma.

ZUWAN TURAWA KASAR HADEJIA 1906 (1)


HADEJIA A YAU! A shekarar 1906 Turawan mulkin mallaka suka ci Hadejia da yaki, Inda yayi sanadiyar mutuwar mutanen Hadejia da dama da kuma wasu daga cikin Turawan. kafin wannan Turawa sun shigo Hadejia ne bayan sun ci Katagum da yaki, koda yake ba yaki sukayi da Katagum ba, sun Meka musu wuya ne ba tare da jayayya ba.

kuma Turawan sun shigo Hadejia ne ta Iyakar kasar Hadejia da Katagum, Inda sukayi sansani a Mai Goriba kusa da Masama. To basu shigo Hadejia ba sai da suka turo Dan leken Asiri wadda ya shigo Hadejia a Matsayin Balarabe mai saida kayan Sarauta Irinsu Alkybba da sauransu. kuma an saukeshi a Gidan Zangoma Wato sarkin Baki.

kuma a haka yayi ta Kewaya Hadejia har ya gane duk sirrin Garin Haka kuma yana kaiwa Sarki kaya yana saye har yasan Sirrin fadar Hadejia.

Wannan dan leken Asirin da yayi shigar Balarabe shine Captain H. C. B. Phillips, Wadda ake ce masa (Mai Tumbi). Kuma kafin suzo Hadejia an basu labarin Garin da kuma Mayakan garin, dan haka shi Captain phillips ya dinga bin Gidajen Jarumai yana Musu alheri a Matsayinsa na dan kasuwa, hakan tasa ya shiga jikinsu sosai kuma suka Amince dashi.