Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Monday, January 26, 2015

TARIHIN KAFUWAR GARIN MAIRAKUMI.







Hadejia A yau!
posted from Bloggeroid

Saturday, January 10, 2015

TARIHIN RAYUWAR ALH. SHU'AIBU HARUNA.


ALHAJI SHU'AIBU HARUNA HADEJIA.
An haifi Alh. Shu'aibu Haruna a cikin garin Hadejia a shekara ta 1-february 1954, yayi makarantar firamare a Matsaro firamare a shekarar1961-1967, yayi makarantar sakandire ta KEDC dake Kano a shekara ta 1969-1974, sannan yayi N. C. E a ATC/ABU Zaria yayi (Degree) a ABU Zaria a inda ya karanci B. ed a Social Studies a shekara ta 1980-1982, Sannan yayiwa kasa shidima wato (NYSC) a Kwara State a shekarar 1979-1980.

Daganan yayi aikin koyarwa a Auyakayi Auyo LGA, a shekara ta 1974-1975, daganan ya koma Bichi Kano State inda yayi aikin koyarwa a shekara ta 1979-1980, Sannan ya rike mukamin (Principal) a Garo dake Kabo LGA a Kano State, a shekara ta 1982-1986, Alh. Shu'aibu Haruna ya sake rike mukamin (Principal) bayan ya koma Kiru LGA Kano State da aikin koyarwa, a cikin shekarar 1986-1991, Sannan yasake rike matsayin (Principal) a Danbatta LGA Kano State a shekara ta 1991-1992, Sannan ya sake rike da matsayin (Principal) a Kaugama LGA Jigawa State, a shekara ta 1992.

Bayan Alh. Shu'aibu Haruna Hadejia ya gama aikin koyarwarsa lafiya cikin nasara da fatan alkairi da abokan aikinsa suka masa, ya rike matsayin (Director General Ministry of Land & Regional Planing Jigawa State) a shekara ta 1992-1993. Sannan ya sake rike matsayin (Dirctor General Budget & Planing Jigawa State) 1993-1994. 

Alh Shu'aibu Haruna Hadejia, ya rike matsayin (Coucilor Hadejia LG Works & Housing) a shekara ta 1994-1996, Sannan ya Zama  (Member Constitutional Amendement) 1999.
Sannan (Chairman Hadejia World Bank Project) sannan (Asst. Sec. Movement for the creation of Hadejia State). Alh. Shu'aibu Haruna gogegge ne a fagen siyasa ya fara harkar siyasa a 1979. NEPU, PRP, NPN, NCPN, NDP, PDP, ANPP, Yanzu kuma yana APC, Kuma (National Delegate) har zuwa yanzu. ganin irin wannan godewa tasa da hakuri irin nasa yasa mutanen Hadejia
suka Tsayar da shi dan Takarar (National House of Assembly) a 2003, NDP. Mai wakiltar Hadejia Auyo da K/Hausa. Alh. Shu'aibu Haruna babban dan kasuwa ne kuma manomi ne, shine mutum na farko da ya fara kawowa kasar Hadejia cigaban da babu wanda ya kawo kasar Hadejia wato Kamfanin Leda mai suna(NAKOWA PLASTIC
LTD) wanda ya samar aiki ga matasan kasar Hadejia, sanadiyyar daukansu aiki da yayi a Kamfaninsa, wanda yanzu sama da mutum 250 suna aiki a karkashin sa, sannan ya
kawo babban cigaba a Harkokin samar da Wayoyin Hannu wato (Handset).Yana da shagunan da ake siyar da wayoyin hannu da dama a cikin garin Hadejiya, wanda mutane sama da 150, suna aiki a shagonan sa. Sannan (Chairman Nakowa Plastics Ltd) & (Pressident Jigawa Chamber of Commerce Mine & Agriculture.

Alh. Shu'aibu Haruna Hadejiya mutum ne mai hakuri da juriya da sanin yakamata. Mutanan Kasar Hadejiya suna maka fatan alkairi Allah ya daukaka rayuwarka Allah ya taimaki zuri'arka baki dayansu. Allah sauran mutanan kasar Hadejia zasuyi koyi da irin halinka. Allah yasake buda maka kasake kawomana wani cigaban kasar Hadejia wanda mutane zasuna karuwa da ita. Amin.

HADEJIA A YAU!

Saturday, December 20, 2014

ZIYARA DA AMFANINTA.

a.

r">
Ziyara wani Nau'i ne na zumunci wanda mutane suke aiwatar da ita domin sada zumunci ga 'yan'uwa da abokan Arziki. zumunci wata irin halayya ce ta kwarai wacce ke sadar da dangantaka ta nasaba tsakanin ’yan'uwa ko bare. Zumunci ne ke kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da fahimtar juna tsakanin al’umma.

Ta hanyoyin da mutum zai bi ya inganta zumunci shine, kaiwa ziyara ga 'yan'uwansa kamar kaka, uba kokuma kanin mahaifi ko kanin mahaifiya da sauransu. Ta haka ne mutum zai gane irin yadda Alaqarsa take da 'yan uwansa na nesa ko na kusa. Haka kuma kowa yana da iya kimar zumuncin da zai gudanar a tsakaninsa da wani. Kamar yadda Hausawa suka ce zumunta a kafa take, to wannan gaskiya ne,domin
kuwa daya daga cikin manyan ginshikan zumunta shi ne ziyartar juna. Idan ka kula da zumunci shike sa mutum ya niki gari zuwa gidan abokinka ko wani dan'uwanka, ko bare musamman domin ganin yadda yake. Wannan ziyara kawai, ita ke haddasa kauna da mutunci mai dorewa a tsakanin al’umma.

A shekarun baya kamar shekara kamar goma zuwa sama,saboda muhimmancin ranar Juma'a,iyaye sukan je da 'ya'yansu gidajen 'yan'uwansu da Abokan Arziki domin gaisawa wanda hakan yana nuna ana nusar da yara ne da kaiwa ziyara ga 'yan uwansu. Harma yara suke kiran wannan ziyara da yawon Juma'a. Amma saboda shagaltar da zuciya irin ta shaidan tasa wannan kyakkyawan Aiki na ziyara ya fara ja baya ga yara harma da manyan a wannan zamani,domin shi bubba yana tunanin ai in yaje zai bada kudi, sannan yaro yana tunanin kar yaje ba'a bashi kudi ba.

Wednesday, December 3, 2014

TAKAITACCEN TARIHIN HASHIM UBALE YUSUF..

Hadejia A yau!

An haifi Hashim Ubale Yusufu a Garun Gabas da ke cikin yankin Karamar Hukumar Mallam Madori ta yanzu, A ranar 21 ga Satumba na shekarar 1956. Ya fara karatunsa a makarantar firamare a nan Garun Gabas inda ya fita da kyakkyawan sakamako a matsayin dalibi mafi kwazo da hazaka Daga nan ya wuce zuwa Sakandaren gwamnati dake Birnin Kudu inda ya yi karatu daga 1969 zuwa 1973, lokacin da ya rubuta jarrawar makarantun sakandare ta Afirka ta Yamma wato WASC.

Ya halarci Makarantar Koyon ilimi mai zurfi ta Kano, wato College of Advanced Studies daga 1973 zuwa 1975, inda ya fita da babbar takardar shaida, wato Higher School Certificate. Daga nan kuma ya sami shiga jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya yi karatun digiri a fannin ilimin harhada magunguna (wato pharmacy) wanda ya gama a shekarar 1981.Bayan ya kammala karatun jami-a, sai sai ya tafi aikin bautar kasa a jihar Imo inda aka tura shi Federal Polytechnic da ke garin Afikpo -Okposi inda ya yi aiki a matsayin mai bayar da magani na wannan makarantar da kuma koyar da darasin chemistry daga 1982 zuwa 1983.Hashim ya fara aiki tun daga matakin karamin ma'aikaci inda a tsawon shekaru ya taka matakai daban daban har zuwa matsayin darakta a hukumar kula da tsaftar abinci da magunguna a Nigeria, da kuma bubban sakatare wato permanent secretary.

Ya fara aiki a shekarar 1974 a matsayinsa na Mataimakin Jami'in gandun daji a karkashin sashen kula da gandun daji na tsohuwar Jihar Kano, sannan daga bisani ya canja aiki zuwa bubban Asibiti na Kano (wanda aka fi sani da asibitin Murtala a yanzu) inda yayi aiki amatsayin jami'i mai bada magani na wucin-gadi a cikin shekarar 1981 da 1982, inda kuma a shekarar 1983 aka daukeshi aiki a karkashin Sashen Kula da ayyukan lafiya kuma aka tura shi Asibitin Murtala da ke Kano a matsayin Jami'in bayar da magani mai daraja ta daya. Daga 1985 zuwa 1987, ya yi aiki a cibiyar sayar da magani ta Lafiya Pharmacy dake garin Hadejia, wadda ta kasance daya daga cikin cibiyoyin sayar da magani da aka bude a wancan lokacin. Bayan daukar lokaci yana aiki karkashin gwamnati,sai ya tsallaka zuwa ma'aikatu masu zaman kansu inda ya yi aiki a kamfanonin sayar da magunguna na NAMCO da kuma ANHEL das u ke cikin binin Kano daga 1987 zuwa 1989. Haka nan ya yi aiki a da hukumar bada tallafin cigaba ta kasar Amurka wato USAID a matsayin jami’in gudanar da ayyuka na kasa karkashin shirin Inganta Lafiyar Iyali (wato Family Health Services).

A shekarar 1989, ya rike mukamin Mai bada shawara a gandun daji na tsohuwar Jihar Kano, sannan daga bisani ya canja aiki zuwa Babban Asibiti na Kano (wanda aka fi sani da asibitin Murtala a yanzu) inda ya yi aiki a matsayin jami'i mai bada magani na wucin-gadi tsakanin 1981 da 1982, inda kuma a shekarar 1983 aka dauke shi aiki karkashin Sashen Kula da ayyukan lafiya kuma aka tura shi Asibitin Murtala da ke Kano a matsayin Jami'in bayar da magani mai daraja ta daya.